Zargin yiwuwar kai harin bam a Filato

Taswirar Najeriya
Image caption Zargin kai harin bam a Filato

Gwamnatin jihar Filato da ke Najeriya ta yi zargin cewa wasu mutane sun shirya kai harin bam a jihar.

Kakakin gwamnatin jihar, Gregory Yenlong ya shaidawa BBC cewa, gwamnatin ta sanar da hukumomin tsaro kan masu shirin kai harin bama-baman amma hukumomin ba su ce komai ba.

Sai dai gwamnatin ta gaza ambatar sunayen mutanen da ta ke zargi da yunkurin kai harin.

A nata bangaren, hukumar rundunar soji ta hadin gwiwa da ke jihar, ta musanta zargin da gwamnatin ta yi.

Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu a jihar Filato, sanadiyar tashe-tashen bama-bamai , inda kuma dubban mutane suka rasa rayukansu a rikicin addini da kabilanci da kuma siyasa.