'Yan tawayen Libya sun kama garin Ras Lanuf

'Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen Libya na murnar nasarar da suka samu

'Yan tawaye a Libiya sun kwace muhimmin garin Ras Lanuf mai tashar mai, yayin da suke dannawa zuwa yamma, domin tinkarar dakarun Kanar Gaddafi.

Wani kwamandan 'yan tawayen ya shaidawa BBC cewa, sojojin Gaddafin suna ta kansu.

Wani wakilin BBC a Ras Lanuf din, ya ce 'yan tawayen na ta yin gaba-gaba cikin gaggawa sosai, akan hanyar da ke gabar teku, tare da goyon bayan kasashen da ke kai hare-hare ta sama, suna lalata tankunan yaki da bindigogin atilare masu yawa, na Kanar Gaddafi.

Ras Lanuf shine gari na baya-bayan nan daga cikin garuruwan da ke gabar tekun Libiyar, wadanda nan da nan suka fada a hannun 'yan tawaye.

Yanzu dai 'yan tawayen sun ce suna sa ran nan da zuwa gobe za su shiga garin Sirte, mahaifar Kanar Gaddafi.