Oauttara bai amince da mai sasanta rikicin Ivory Coast ba

Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto AFP

Mutumin da kasashen duniya suka amince da shi a matsayin shugaban kasar Ivory Coast, Allasane Oauttara, ya ki amincewa da mutumin da kungiyar tarayyar Afrika ta zaba, a matsayin mai shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.

Kungiyar dai ta ba da sunan tsohon ministan harkokin wajen Cape Verde, Jose Brito a matsayin wakilinta a rikicin siyasar ivory Coast.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin dillanci labarai na kasar Faransa ya fitar, Mr Oauttara ya zargi Mr Brito da cewa yana da kusanci sosai da Mr Laurent Gbagbo, mutumin da ya ki amincewa da shan kaye a zaben kasar.

Kazalika a birinin Abidjan dubun dubatar magoya bayan Mr Gbagbo, sun gudanar da wani gangami a gaban fadar shugaban kasar a daren jiya .