Wata sabuwa a tashar Fukushima

Tashar makamashi ta Fukushima Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tashar makamashi ta Fukushima

Masu kula da tashar makamashin nukiliya ta Fukushima, wadda ta kassare a sakamakon girgizar kasa da mahaukaciyar ambaliyar ruwan nan ta Tsunami, sun ce a karon farko an samu ruwan da ke fitar da tururun nukiliya a waje da daya daga cikin ginin da ke dauke da tukunyar nukiliyar.

An samu ruwan ne mai fitar da tururun nukiliyar da ba'a taba samu ba kawo yanzu, a wata hanyar karkashin kasa da ke dauke da bututu a gab da bakin teku.

Rahotannin da aka samu sun ce, akwai alamun tururun nukiliyar ya fito ne daga bututun makamashin nukiliyar da ya narke, wanda kuma ya taba ruwan.