Rawar da 'yan jarida za su taka a zaben Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Rawar da 'yan jarida za su taka a zaben Najeriya

Majalisar 'yan jarida a Najeriya ta gabatar da wani taro a Kaduna kan irin rawar da 'yan jarida za su taka wajen ganin an gudanar da zaben 2011 lafiya.

Majalisar ta ce ya kamata 'yan jaridu su guji aikewa da rahotannin da za su iya tayar da hankula.

Ta kara da cewa hakan zai faru ne kawai idan 'yan jaridar suka gudanar da ayyukansu bisa yin biyayya ga ka'idojin aikinsu.

'Yan jaridar Najeriya dai na fuskantar kalu-bale da dama wajen gudanar da ayyukansu.