'Yan tawayen Libya sun gamu da cikas

'Yan tawayen kasar Libya, sun gamu da cikas a hannun dakarun gwamnatin kasar, a kokarin da suke yi na dannawa zuwa yammacin kasar, ta gefen bakin gabar teku, zuwa yankunan da sojojin Gaddafi suka kama kasa a bayan garin Bin Jawad.

Wani wakilin BBC ya ce 'yan tawaye da dama a dimauce sun janye daga cikin garin, suna cewar sojojin Gaddafin na maida martani.

Dama wani kwantan baunar da sojojin gwamnatin suka yi ya kai ga dakaar da dannawar da 'yan tawayen ke yi yamma kadan da birin na Bin Jawad, wanda ke da nisan gaske da birnin Sirte, - birnin da 'yan tawayen suka yi ikrarin sun kame.

A sakamakon hare-haren da kasashen waje ke kaiwa 'yan tawayen sun kame garuruwan Brega da Ras Lanuf.

Wani dan tawaye ya bayyana cewar lokacin da suka isa wadannan garuruwa babu wata matsala da suka fuskanta.