Mun kame mahaifar Gaddafi, in ji 'yan tawayen Libya

'Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen sun kame garin Sirte

'Yan tawayen kasar Libya sun ce sun kame garin Sirte, inda nan ne mahaifar kanal Gaddafi.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta wadda ta tabbatar da hakan.

'Yan tawayen na ci gaba da matsawa zuwa garuruwan da ke hannun masu goyon bayan Gaddafi.

Da fari dai an ji fashewar wani abu a Tripoli, babban birnin kasar.

Kuma gwamnatin kasar ta ce, kungiyar kawancen NATO na son durkusar da kasar ne kawai.

Ibrahim Musa shi ne kakakin gwamnatin, ya ce NATO na son kashe 'yan kasar ne, kana su maida su bayi.