Hanyar magance karancin abinci a Niger

Zababben shugaban Niger Mohammadou Issoufou
Image caption Zababben shugaban Niger Mohammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar, yau ne hukumomin kasar tare da tallaffin kasashe masu hannu da shuni, suka bude wani zaman muhawara na kwanaki hudu, don lalubo hanyoyin magance matsalar karancin abinci ko yunwa da ke aukawa a kasar a kai a kai.

Manufar muhawarar ita ce samar da hanyoyin yaki da yunwa, da samun ci gaba mai dorewa ta fannonin noma da kiwo.

Duk da samun damina mai albarka a bana, yanzu haka dai mutane fiye da milyan biyu ne ke a cikin halin bukatar agajin abinci a Nijar din.