Zaben 2011: 'Yan adawa daga arewacin Najeriya na ganawa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A yayin da zaben shekarar 2011 a Najeriya yake kawo jiki, rahotanni daga Najeriyar na nuna cewa 'yan takarar shugabancin kasar na jamiyyar ACN, da ANPP da CPC na ganawa a kokarin fitar da dan takara daya daga cikin su.

Wanda suka yanke shawara a kai shi ne zai fafata tare da shugaban kasar Goodluck Jonathan daga jamiyyar PDP.

A baya dai kokarin da jamiyyun suka yi na fitar da dan takara daya daga cikin 'yan takara uku na jamiyyun adawar bai yi nasara ba, a bisa wasu banbance-banbance da ke tasakaninsu.