Mutane 78 sun mutu a Yemen sakamakon fashewar nakiya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wata shirgegiyar nakiya da ta yi bindiga a wata ma'aikatar kera makamai a kasar Yemen, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla saba'in da takwas.

An ji Karar fashewar nakiyar wadda ta yi bindiga a garin Jaar na kudancin kasar, daga nisan kilomita goma sha biyar, ta kuma jiwa wasu mutane da dama raunika.

Nakiyar ta fashe ne a yayin da wasu mutanen garin suka je kwasar ganima a ma'aikatar, kwana daya bayan da wasu mutane dauke da makamai suka kame ma'aikatar.

A can Sana'a kuwa, masu zanga zangar nuna kyamar gwamnati na ci gaba da zaman dirshan a dandalin Taghyeer.