Amurka ta nemi gafara wajen Afghanistan

Sojojin Amurka a Afghanistan
Image caption Amurka ta nemi gafara daga Afghanistan

Ma'aikatar tsaron Amurka ta sake neman afuwa bayan da wata mujalla a kasar ta wallafa hotunan da suka nuna sojojin kasar a tsaye kusa da gawarwakin fararen hula a Afghanistan.

Ta ce hotunan da mujallar Rolling Stone ta wallafa abubuwa ne masu tayar da hankali , kuma abu ne da ya sabawa manufofin rundunar sojin kasar.

Daya daga cikin hotunan ya nuna wani sojin Amurka yana murmushi kuma ya daga yatsansa sama, a lokacin da ya gyara kan wani mamaci domin su dauki hoto.

Batun dai ya harzuka mutane da dama a kasar Afghanistan.