Harbe-harben bingogi sun watsa taron ANPP a Borno

'Yan sanda a Maiduguri
Image caption Ana fatan kwanciyar hankali lokacin zabe

Kimanin mutane hudu sun hallaka, kuma da yawa sun jikkata, a lokacin wani turmutsitsin da aka yi a Dandalin Ramat da ke Maiduguri, yayin da ake shirin gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar ANPP shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Mutanen da suka hallara sun yi ta kansu ne, yayin da aka rika jin karar harbe-harben bindiga.

A wani gefen kuma, rundunar 'yan sandan jahar Bornon ta kama wasu mutane biyu, kamar yadda ta ce, dauke da bama bamai, wadanda take zargin suna shirin danawa ne a Dandalin na Ramat.

A makon jiya dai takaddama ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Bornon, Ali Modu Sheriff, da bangaren dan takarar ANPPn, Malam Ibrahim Shekarau, bayan da gwamnan ya ce bai shirya karbar bakuncin taron gangamin ba, jim kadan da isowar dan takarar.