Japan na cikin shirin ko-ta-kwana

Naoto Kan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Naoto Kan

Firayi ministan Japan Naoto Kan ya ce gwamnatinsa na cikin shirin ko-ta-kwana kan tashar nukiliyar Fukushima da ta lalace .

Jami'ai sun ce an gano sinadarin Plutonium a karkashin kasar da ke yankin kuma ruwan da ke hana tururin nukiliyar ya rika yoyo daga wata tukunyar da ke cikin tashar nukiliyar.

Mista Kan ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa a halin da ake ciki ba za'a iya sanin yadda abubuwa za su kasance nan gaba ba.

Sai dai ya ce gwamnatinsa na kokarin ganin ta shawo kan matsalar cikin gaggawa