Taron London ya kafa kwamiti a kan Libya

Firaministan Birtaniya, David Cameron Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Firaministan Birtaniya, David Cameron

Taron kasashe kan Libya ya amince da kafa wani kwamitin tuntubar juna da ya hada da kasashen Larabawa, domin yin aiki tare wajen taimaka wa Libya, bayan shudewar gwamnatin Gaddafi.

Kasar Qatar ta ce za ta karbi bakuncin taron kwamitin na farko.

Sakataran kula da harkokin wajen Birtaniya, William Hague, ya fadi a wajen taron da sukai yau a nan London cewa Gaddafi ya rasa halaccin da yake da shi na mulki.

Kuma za a dora alhakin duk wata ta'asar da aka yi a kasar a kansa.

Ita ma Sakatariyar Harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce za su ci gaba da daukar matakin soji kan Libya:

Ta ce za a ci gaba da daukar wannan matakin sojojin har sai Gaddafi ya bi ka'idojin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1973, ya daina kai hari kan fararen hula, ya kuma janye sojojinsa daga inda suka shiga ta karfin tsiya.