Kasar Libya na da hadari, in ji Obama

Barack Obama Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Obama ya ce libya na da hadari

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce Libya za ta ci gaba da kasancewa kasa mai hadari idan har Gaddafi bai sauka daga kan mulki ba.

Sai dai Mista Obama ya nanata cewa fadada aikin sojojin kasashen duniya daga kare fararen hula zuwa kafa sabuwar gwamnati a kasar, zai kasance wani kuskure saboda zai janyo baraka tsakanin kasashen da suka kulla wannan kawance .

Ya ce yana da tabbacin cewa matakin mika jagorancin kaiwa Libya hari daga Amurka zuwa ga kawayenta zai cigaba da matsawa dakarun Gaddafi lamba.

Mista Obama ya shaidawa Amurkawan da ke adawa da shigar kasar cikin harin da ake kaiwa Libya cewa, ya ba da umarnin shiga kasar ne da zummar kare 'yan kasar.