Jama'a na zanga-zanga a Dengi, jihar Filato

Hakkin mallakar hoto AFP

Dubban mutane suna ci gaba da zanga-zanga a garin Dengi, hedkwatar karamar hukumar Kanam a jahar Filato, saboda matakin da gwamnatin jihar ta dauka, na sauke shugaban karamar hukumar.

Tun ranar Juma'ar da ta wuce ce aka soma zanga zangar.

A cewar gwamnatin Filato, ta sauke shugaban karamar hukumar ta Kanam ne, Barista Sale Muhammad, tare da takwaran aikinsa na Langtang ta Kudu, Hitler Dadi, sabo da zargin rashin gaskiya.

Amma mutanen biyu sun ce, matakin na da nasaba da siyasa, saboda su 'yan jam'iyyar adawa ta Labour ne, wadda mataimakiyar gwamna, Mrs Pauline Tallen, ke wa takarar gwamna