Burtaniya ta yi wa Najeriya fatan zabe nagari

Sarauniyar Ingila
Image caption Sarauniyar Ingila

Burtaniya ta yiwa Najeriya fatan alheri, yayin da ake shirin fara gudanar da zabubuka a kasar.

Jakadan Burtaniya a Najeriya Andrew ne ya bayyana hakan, yana mai fatan zaben zai zama sahihi, ta yadda jama'ar Najeriyar, da ma sauran kasashen duniya, za su yi na'am da shi.

Ya ce: " A ranar Asabar, 'yan Najeriya za su koma rumfunan zabe, dauke da fata mai yawa, da kuma damuwa a zuciyoyinsu. Shin za a amince da zaben su, a kirga, a kuma mutunta? Shin kuri'unsu za su yi tasiri? Shin wadannan tashe-tashen hankulan da ake fama da su za su ci gaba?

Jakadan Burtaniyan ya kuma yaba wa shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru jega saboda namijin kokarin da ya ce yana yi.

Ya kuma bayyana farin cikinsa dangane da sanya hannu a kan alkawarin gudanar zabe cikin mutunci da jam'iyyun siyasar kasar suka yi.

Mr Andrew ya kuma ce, zabe, shugabanci na gari, ci gaba, habakar tattalin arziki da sauransu ba su kadai warwara ga matsalolin da Najeriya ke fama da su ba, amma suna daga cikin ginshikan ci gaba.