'Ana take hakkin dan adam a Najeriya'

Tambarin kungiyar Human Rights Watch
Image caption Kungiyar Human Right Watch ta zargi Najeriya

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta Human Rights Watch ta zargi hukumomi a Najeriya da aikata laifukan keta hakkin bil-adama.

Kungiyar ta ce kasar na fuskantar manyan kalubale na kare hakkin bil-adama.

A cewar kungiyar, jami'an tsaro da kuma gwamnatoci a Najeriya na matukar keta hakkin dan Adam, lamarin da kan kai ga asarar dimbin rayukan 'yan kasar da kuma tsare mutane ba gaira ba dalili.

Kungiyar a cikin rahotonta kan Najeriya, wanda ta yi wa lakabi da 'Ajandar Kare Hakkin Bil-Adama ga 'yan takara a zaben Nijeriya na 2011', ta ce wajibi ne 'yan takara su maida hankali ga batun kare hakkin bil-adama yayin yakin neman zabensu, da kuma bayan sun ci zaben.