Shugaba Jonathan ya yi muhawara shi kadai

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya halarci wata muhawara shi kadai a taron muhawarar da wata kungiya mai suna Nigeria Debate Group ta shirya wa 'yan takarar shugaban kasar a zabe mai zuwa.

Shugaba Goodluck Jonathan yana muhawarar da kansa ne sakamakon kauracewar da abokan hamayyarsa na jam'iyyun adawa na ACN, da CPC da kuma ANPP suka yi.

A baya an yi ta cece ku ce a kan kauracewa muhawarar farko da gidan talabijin na NN24 ya shirya, inda manyan abokan hamayyar sa na ACN, da CPC da kuma ANNP suka halarta amma shugaba Jonathan ya kaurace wa muhawarar.

Wannan ya sa aka yi ta jefa masa maganganun cewa tsoro ne ya hana shi zuwa. Amma ya bayyana a wata muhawarar sai dai sauran 'yan takarar ba su halarta ba.

NEDG

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi muhawara shi kadai a taron muhawarar da wata kungiya mai suna Nigeria Election Debate Group NEDG ta shirya wa 'yan takarar shugaban kasar a zabe mai zuwa.

Shugaban ya fara ne da bayyana dalilinsa na kin halartar muhawarar da gidan Talabijin na NN24 ya shirya, yana mai cewa ba ya kasar a lokacin da aka gabatar da muhawarar.

Yace: "Fiye da kungiyoyi goma daban-daban da suka hadar da kafofin yada labarai da kungiyoyi masu zaman kansu ne suka tuntube ni domin gudanar da muhawara, amma abin da muka yi tunani shi ne, shugaban kasa ba shi da damar halartar muhawarori dabam-daban, a don haka muka bukaci kungiyar Nigeria Election Debate Group da ta shirya muhawara daya da za ta kunshi kafofin yada labarai dabam-daban da za su watsa ga al'ummar kasa.

Ko wannan uzurin nasa zai gamsar da masu zabe da abokan hamayyarsa wani abu ne daban, amma ganin cewa ya mayar da martani ga rashin halartar muhawarar ya nuna cewa ya ji sukar da aka yi masa.

A muhawarar da shugaban ya yi shi kadai, ya bayyana cewa zai ci gaba da ayyukan da ya fara tare da marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa 'Yar'adua.

Ya ce batun samar da wutar lantarki shi ne abin da zai sa gaba idan 'yan Najeriya suka kara bashi wani wa'adin na shekaru hudu masu zuwa, ya ce zai tabbatar da daidaituwar lantarki, sai dai shugaban kasar bai bayyana yadda zai tabbatar da daidaiton ba.

Shugaba Jonathan ya kuma ce ba zai nuna bambanci tsakanin 'yan kasar ba, ba kuma zai kawo wasu manufofi da za su karfafi wani bangare yayinda za su musguna wa dayan.

Sai dai wasu na ganin muhawarar ta yau wadda shugaba Jonathan ya yi shi kadai da kansa wata dama ce da aka bashi na kitse yakin neman zabensa, inda ya yi kidansa ya yi rawarsa shi kadai.

Mallam Ibrahim Modibbo na kungiyar yakin neman zaben Mallam Nuhu Ribadu na jam'iyyar ACN ya bayyana cewa muhawarar da aka gudanar wasan yara ne, kuma maganganun da shugaban ya yi rudu ne, kuma duk da zarafin da ya samu a kafofin yada labaran gwamnati ya kasa bayyana wa 'yan Najeriya abin da ya yi ko zai yi musu don kawo sauyi a halin kuncin da suke ciki a yanzu, abinda ya nuna cewa babu wani abin kirki da zai iya tabukawa a mulkin kasar.

Shi ma Mallam Sule Yau Sule na kungiyar yakin neman zaben Mallam Ibrahim Shekarau na jam'iyyar ANPP, ya ce shugaban yana tsoron gwabzawa ne da sauran 'yan takarar don kada su kunyata shi, shi ya sa ya kauracewa waccan muhawarar ya zabi ya yi kidansa da rawarsa shi kadai.