'Yan Tawayen Libya na ci gaba da ja da baya

'yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan tawaye a kasar Libya na ci gaba da ja da baya sakamakon zafafa hare-haren da sojojin Gaddafi ke yi suna kara nausawa gabashin kasar.

Daruruwan mayakan 'yan tawaye sun tsere daga garin Brega mai arzikin man fetur, bayan sun guje daga sauran birane da ke bakin gaba a cikin sa'oi ashirin da hudu da suka gabata.

Wani wakilin BBC ya ce sojojin Kanal Gaddafi sun fara amfani da irin dabarun da sojojin 'yan tawaye suka yi amfani da su na tuka motoci da suke da budadden baya makare da makamai, abinda ya sanya abu ne mai wuya sojojin kawance su gane su su kuma jefa musu bam.

Tun da farko dai ministan kula da harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov yace dakarun kasashen waje dake Libya basu da ikon baiwa 'yan tawayen dake fada da dakarun Kanal Gaddafi makamai.

Mr. Lavrov yace Rasha ta amince da matsayin NATO ne na cewa aikinta shi ne na kare jama'ar kasar bawai ba su makamai ba.

Minsitan harkokin wajen Rasahan na mayar da martani ne ga jawabin shugaban Amurka Barack Obama wanda ya ce mai yiwuwa kasarsa ta taimakawa 'yan tawayen Libya da makamai don ci gaba da gwagwarmayar da suke yi da dakarun Gaddafi.

A wasu jerin hirarraki da wani gidan talabijin din Amurka, shugaba Obama ya ce har yanzu yana nazari kan irin taimakon da 'yan tawayen Libya ke bukata daga wajensa.

Ya kara da cewa, takunkumi da kuma hare-haren da ake kaiwa dakarun Gaddafi sun yi matukar illa a gare shi.

Ya ce:''Ba ni da shakkun cewa, idan muna son shiga da makamai Libya, abu ne mai yiwuwa''.