Shugaban Syria zai yi jawabi ga 'yan kasar

Shugaban Syria Bashir Assad
Image caption Assad zai yi jawabi ga 'yan kasar

Idan an jima a yau ne ake sa ran shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad zai yi jawabi ga 'yan kasar.

Rahotanni na cewa zai bayar da sanarwar janye dokar ta-bacin da ta yi shekaru hamsin tana aiki a kasar.

Sanarwar na zuwa ne bayan kwashe makonni biyu ana zanga-zanga a kasar ta Syria, inda aka kashe mutane fiye da sittin.

Amurka ta bayyana damuwarta game da lamarin.