Ana gwabza kazamin fada a birnin Abidjan

Dakaru maso goyon bayan Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakaru masu goyon bayan Alassane Ouattara

Dakarun dake biyayya ga mutumen da kasashen duniya suka dauka a matsayin zababben shugaban kasar Cote d'Voire, Alassane Ouattara, sun shiga babban birnin kasuwancin kasar, Abidjan, inda Laurent Gbagbo, mutumin da ya ki sauka daga kan karagar mulki yake da karfi.

Mazauna unguwannin dake kusa da gidan talabijin na kasar sun ruwaito cewa, suna jin karar harbe harbe ba kakkautawa, yayin da a wasu wuraren kuma dakarun soji ke tserewa suna komawa bangaren Alassane Ouattara.

A waje daya, kuma wasu 'yan sanda ko kuma jandarma na Cote d'Voire din dake gujewa fadan, sun tsallaka sun shiga Ghana, inda suka mika kansu ga hukumomin tsaron kasar.

Rahotanni sun ce dakarun Majalisar Dinkin Duniya masu aikin kiyaye zaman lafiya Cote d'Ivoire, sune ke iko da filin saukar jiragen saman birnin na Abidjan.