Dakarun Alassane Ouattara sun shiga Abidjan

Dakarun dake biyaya ga Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dakarun dake biyaya ga Alassane Ouattara

Dakarun da ke biyaya ga mutumen da kasashen duniya suka amince da shi a matsayin shugaban Cote D'Ivoire, Alassane Ouattara, sun shiga birnin Abidjan.

Wani wakilin BBC a birnin, ya ce ana mummunar musayar wuta a kewayen Ginin talabijin din kasar tsakanin dakarun dake biyaya ga Alassane Ouattara da wadanda ke goyon bayan Laurent Gbagbo, wanda ya ki ya sauka daga kan karagar mulki, bayan zaben da aka yi a bara.

Mataimakin Babban Hafsan rundinar sojojin kasar, wadda har yanzu ke goyon bayan Mr Gbagbo, ya koma bangaren Mr Ouattara.

Tun farko kuma, Babban Hafsan rundinar sojin kasar, Janar Phillippe Mangou, ya nemi mafaka a gidan Jakadan Afrika ta Kudu a birnin na Abidjan.