William Hague: ba mu ba Moussa Koussa kariya ba

William Hague, Sakataren harkokin wajen Birtaniya Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ba mu ba MoussaKoussa kariya ba.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya ce zuwan ministan harkokin wajen kasar Libya,Moussa Koussa, Birtaniya, ya nuna cewa gwamnatin Kanar Gaddafi ta ruguje, kuma tana fuskantar matsin lamba da rarrabuwar kawuna a cikinta.

Mr Hague ya ce su na karfafawa mutanen Gaddafi gwiwar cewa, su rabu da shi, su rungumi sabuwar makoma ga Libya, wadda ta sakarwa harkokin siyasa mara, tare da kawo sauye sauye masu maana da alummar Libya ke hankoron samu.

Mr Koussa ya isa birnin London ne a daren ranar Laraba daga kasar Tunisia, yana mai cewa yanzu ba ya so ya yiwa Kanar Gaddafi aiki.

Sai dai Mr Hague ya dage kan cewa Birtaniya ba ta Mr Koussa kariya daga gurfana a gaban sharia ba.