NATO ba za ta ba 'yan tawayen Libiya makamai ba

Anders Fogh Rasmussen Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Anders Fogh Rasmussen

Babban Sakataren kungiyar kawancen tsaron NATO, Anders Fogh Rasmussen ya ce yana adawa da batun samarwa 'yan tawayen Libya da makamai. Ya ce kungiyar NATO ta je Libya ne domin kare fararen hula, ba wai ba su makamai ba.

Matsayin Mr Rasmussen dai ya ci karo da manufar Amirka da Birtaniya, wadanda ba su fidda tsamannin samar da kamamai ga 'yan tawayen na Libya ba. Kalaman nasa sun zo ne yayin da 'yan tawayen Libyar suka fuskanci koma-baya a fadan da ake suke yi da dakarun da ke biyaya ga gwamnatin Kanar Gaddafi, wadanda ke ta yi masu luguden wuta.