An fara baza jami'an tsaro a Nijeria saboda zabe

Wasu jami'an tsaro a Nijeriya
Image caption Wasu jami'an tsaro a Nijeriya

Yayin da ya rage kwanaki biyu a fara babban zabe a Najeriya, yanzu haka hukumomi sun soma baza jami'an tsaro sosai a duk fadin kasar da nufin sa-ido a aikin. Matsalar tsaro tana ci gaba da janyo fargaba da kuma muhawara a tsakanin 'yan kasar, yayin da hukumomi kuma ke cewa suna daukar dukkan matakai da suka kamata domin katse hanzarin duk wata barazana ta tsaro a yayin zabukan.

A kasar dai an sha fuskantar tashe-tashen hankula na kabilanci da addini da kuma siyasa a wasu sassa na kasar, baya ga matsalar 'yan bangar siyasa da kan kai ga hasarar dimbin rayuka.