Fada ya yi zafi a fadar shugaban Ivory Coast

Sojojin Ouattara na shirya kai hari kan fadar shugaban kasa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojojin Ouattara na shirya kai hari kan fadar shugaban kasa

Yayinda fafutukar kwace iko da kasar Ivory Coast ta shiga mataki na karshe, rahotanni sun ce dakarun da ke biyayya ga wanda kasashen duniya suka yi ittifakin cewa shi ne shugaban kasar, Alassane Ouattara, na gwabza kazamin fada daura da gidan abokin hamayyarsa, Laurent Gbagbo, a Abidjan, birni mafi girma a kasar.

A 'yan kwanaki kadan din da suka wuce ne dai dakarun Mista Ouattara suka kwace iko a akasarin kasar.

Rahotannin sun ce dakarun na Mista Ouattara suna fuskantar turjiya daga zaratan sojojin da ke baiwa Laurent Gbagbo kariya a kokarin da suke yi na kwace iko da fadar shugaban kasar.

Mista Ouattara dai ya ce dakarunsa sun yiwa Mista Gbagbo—wanda ya ki yarda ya mika mulki—kofar rago.

“A yau dakarun sun yiwa Abidjan tsinke”, in ji Mista Ouattara.

Ya kuma kara da cewa, “Ina kira ga dukkan wadanda suke kila-wa-kala—janar-janar ne ko manyan jami'an soja, ko ma kananan sojoji—ku mika wuya ku yiwa kasar ku biyayya, ku kuma dawo kan hanyar bin doka.

“Har yanzu kuna da sauran lokaci don ku hade da 'yan uwanku sojojin jamhuriya”.

Mazauna birnin na Abidjan dai sun bayar da labarin jin karar manyan bindigogi a yankin da fadar shugaban kasar ta ke da kuma kewayen gidan talabijin na kasar, wanda a baya dakarun Mista Ouattara suka ce sun kwace.

Karin bayani