Mata dubu, jarirai dubu biyu na mutuwa kullum

Ungozoma a bakin aiki Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ungozoma a bakin aiki

Wani rahoton kungiyar bayar da agajin nan ta Save the Children ya gano cewa a duk fadin duniya, mace daya cikin uku na haihuwa ne ba tare da ungozoma ba.

Hakan kuma, a cewar rahoton, wani lokaci ya kan kai ga asarar ran uwa ko jaririn.

Rahoton ya kuma kara da cewa a kowacce rana mata dubu daya da kuma jarirai dubu biyu ne ke mutuwa sakamakon tangardar da ta shafi haihuwa wadda kuma za a iya kaucewa aukuwarta.

Rahoton na kungiyar Save the Children ya kuma bayyana cewa akwai matukar karancin ma'aikatan kiwon lafiya masu kwarewa wajen karbar haihuwa.