Zanga zanga a Ghana akan kisan sarkin Dagomba

Taswirar Ghana
Image caption Taswirar Ghana

A Ghana, wasu daruruwan 'yan kabilar Dagomba dake goyon bayan gidan sarautar Andani sun yi zanga zanga yau a birnin Accra, don neman a hukunta mutanen da suka kashe wani Basarakensu.

Masu zanga zangar suna so ne su matsawa gwamnatin shugaba John Atta Mills lamba, don ganin an sake gurfanar da wasu mutane 15 a gaban kotu, bayan da wata babbar kotu dake birnin Accra ta wanke su a ranar Talatar da ta wuce.

Ana zargin mutanen ne da yi wa babban sarkin kabilar Dagombar, Yana Yakubu Andani kisan gilla, a shekara ta 2002.

Dukan wadanda ake tuhumar magoya bayan gidan sarautar Abdu ne dake hamayya da gidan sarautar Andani, inda marigayin sarkin ya fito.