'Tsoffin 'yan tawayen Nijar na fafatawa a Libiya'

Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto APTN
Image caption Kanar Gaddafi

Wani tsohon madugun 'yan tawaye a jamhuriyar Nijar ya tabbatar cewa, akwai tsoffin 'yan tawayen da yanzu haka suke tallafawa dakarun Kanar Gaddafi a Libiya, a fafatawar da yake yi da 'yan tawayen kasarsa.

Da ma a Nijar din ana ta rade-radin cewa akwai wasu tsaffin 'yan tawaye Abzinawa dake marawa sojojin Kanar Gaddafi baya.

A hirar da yayi da manema labarai a yau, wani tsohon kakakin kungiyoyin tawaye na arewacin kasar, Malam Saidou Kaocen Maiga, ya tabbatar cewa, yanzu haka akwai tsoffin mayakan fagen daga a Libiya.

A cewarsa ya kamata gwamnatin Nijar ta dauki matakin maido su kasar, saboda a yanzu haka akwai tsoffin 'yan tawaye Abzinawa da Tubawa su fiye da dubu hudu, wadanda suka kwance damarar yaki a shekara ta 2009, amma ba wani tallafi da hukumomin Nijar ke basu.

Malam Saidou Kaocen Maiga ya ce, tsoffin 'yan tawayen sun koma sojan haya ne a Libiyar, saboda albashi mai tsokar da Kanar Gaddafi ke basu.

Gwamnatin Nijar ta ce ba ta da masaniya game da wannan labarin.