Mutane 15 sun halaka a tarzomar Yemen

Mummunar zanga zanga a Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mummunar zanga zanga a Yemen

Jami'an tsaro a kasar Yemen sun harba harsasai da hayaki mai sa hawaye, domin tarwatsa dubban masu zanga-zangar da ke neman shugaba Ali Abdullah Saleh ya sauka daga mulki.

Jami'an asibiti sun ce akalla mutane 15 aka kashe a birnin Taiz, yayin da mutane da dama su ka jikkata.

A birnin Hudaida na gabar kogin Maliya, daruruwan masu zanga-zanga sun jikkata sanadiyyar dauki-ba-dadi da jami'an tsaro, yayin da su ka yi kokarin yin jerin gwano zuwa wata fadar shugaban kasa.

Wasu rahotannin kuma na cewa, jami'an tsaron sun labe a kan rufin gidaje su na yi wa masu zanga-zangar harbin dauki dai-dai.