Ma'aikatar tsaron Burtaniya ta sarara

Sakataren tsaro na burtaniya, Liam Fox
Image caption Sakataren tsaro na burtaniya, Liam Fox

Ma'aikatar tsaron Burtaniya ta samu sararawa dangane da gibin dala biliyan daya da dubu dari shida a kasafin kudinta.

Ma'aikatar tsaron dai ta samu wannan sararawar ne sakamakon abin da ake cewa kira ne da manyan hafsoshin soja suka yi a kan gwamnati ta sake tunani dangane da yadda shirinta na tsuke bakin aljihu zai shafi sha'anin tsaro, musamman ma sakamakon rikicin da ake yi a Libya.

Wadansu daga cikin kudaden da ma’aikatar tsaron za ta kashe dai za su fito ne daga aljihun ma’aikatar kudi ba daga kasafin kudinta ba, musamman kudaden alawus na mayakan da ke fagen daga.

Tuni dai masu sharhi ke cewa kasafin kudin na ma'aikatar tsaron Burtaniya zai sake yin karo da tsuke bakin aljihu a badi.