Ana ci gaba da gwabza fada a Ivory Coast

Sojojin Alassane Ouattara Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojojin Alassane Ouattara

Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a birni mafi girma na kasar Ivory Coast, Abidjan.

Yankin da Laurent Gbagbo, wanda ya kekasa kasa ya ki mika mulki, ya ke iko da shi dai ya ragu matuka zuwa unguwar da gidansa ya ke a birnin na Abidjan.

Sai dai yayin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun da ke goyon bayan Alassane Ouattara, wanda kasashen duniya suka yi ittifakin cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da kuma dakarun da ke tsaron Mista Gbagbo, Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da nuna damuwa dangane da yadda ta ce bangarorin biyu na keta hakkokin bil Adama.

A wadansu sassan kasar ma an bayar da rahoton tashe-tashen hankulan da suka jawo mutane da dama suka rasa rayukansu.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akalla mutane dari takwas ne suka rasa rayukansu a garin Doueké.

Kungiyar ta ce yawan gawarwarkin da jami'anta suka gani ya kidima su.

Ta kuma ce jami’anta a kasar ta Ivory Coast na ci gaba da bincike a kan al’amarin.

Kungiyar ta Red Cross ta kuma yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna su mutunta dokokin kasa-da-kasa a kan kare hakkin bil Adama.

Karin bayani