Fada ya sake farkewa a Ivory Coast

Fada ya sake barkewa nan da can a birnin Abidjan na Kot Divuwa, tsakanin magoya bayan shugabannin kasar guda biyu.

Wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Abidjan, Hamadou Toure, ya ce ana ta musayar wuta.

Ya ce, "Muna karar manyan bindigogi da kuma 'yan harbe-harbe kusa da fadar shugaban kasa, a yanzu din nan da muke magana. Don haka ana cikin zaman dardar."

An ba da rahoton dakarun Alassane Ouattara suna shirin kara yunkurawa zuwa fadar Shugaban Kasa, sun kuma kafa dokar hana yawo a birnin.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Faransa sun karbi ikon filin jirgin sama daga hannun Majalisar Dinkuniya.

Faransar ta kuma kara yawan sojinta da dakaru dari ukku.

Rahotanni sun kuma ce an raunata sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya guda hudu a yinin jiya Asabar.

A akasarin birnin dai an sanya dokar hana fitar dare ko da yake ba a san hakikanin wanda ke tabbatar da bin dokar ba.

Wani mazaunin birnin ya shaidawa BBC cewa gungun mutane dauke da makamai na karakaina a kan tituna.

“Ina iya ganin wadansu mutane farar hula su hudu ta taga, wadanda suka rufe fuskokinsu, dauke da bindigogin Kalashnikov”, in ji mutumin, wanda ba ya so a ambaci sunansa.

Ya kara da cewa, “Ga wadansu can kuma [ina hango su] su takwas sanye da wando jeans suna gangarowa—akasarinsu suna rike da bindigogi”.

Dakarun Mista Ouattara sun ce suna fadan karshe ne, amma ga alamu suna fuskantar matsananciyar turjiya.

Karin bayani