Shugaban Kazakhstan zai sake tsayawa zabe

Nursultan Nazarbayev Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Kazakhstan, Nursultan Nazarbayev

Mutumin da yake mulkin kasar Kazakhstan tsawon fiye da shekaru ashirin, wato Nursultan Nazarbayev, zai sake tsayawa takarar zaben shugaban kasar da ake yi yau Lahadi—kuma dukkan alamu na nuna cewa zai sake lashe zaben.

A karkashin wadansu sauye-sauyen da aka yiwa kundin tsarin mulkin kasar dai a shekarar 2007, Mista Nazarbayev yana da damar tsayawa takarar shugabancin kasar ko sau nawa ya ga dama.

Sai dai manyan jam’iyyun adawar kasar sun ce ba a ba su isasshen lokaci don su shiryawa zaben ba.

A cewarsu babu alamun adalci a zaben, don haka suka yi kira a kaurace masa.

A kasar ta Kazakhstan dai ba a taba yin zaben da masu sa ido masu zaman kansu suka shaida cewa yana da sahihanci ba.