An sabunta: 1 ga Aprilu, 2011 - An wallafa a 19:46 GMT

Fada ya yi zafi a fadar shugaban Ivory Coast

Ivory Coast

Fada ya yi kamari a 'yan kwanakin nan a Ivory Coast

Yayinda fafutukar kwace iko da kasar Ivory Coast ta shiga mataki na karshe, rahotanni sun ce dakarun da ke biyayya ga wanda kasashen duniya suka yi ittifakin cewa shi ne shugaban kasar, Alassane Ouattara, na gwabza kazamin fada daura da gidan abokin hamayyarsa, Laurent Gbagbo, a Abidjan, birni mafi girma a kasar.

A 'yan kwanaki kadan din da suka wuce ne dai dakarun Mista Ouattara suka kwace iko a akasarin kasar.

Rahotannin sun ce dakarun na Mista Ouattara suna fuskantar turjiya daga zaratan sojojin da ke baiwa Laurent Gbagbo kariya a kokarin da suke yi na kwace iko da fadar shugaban kasar.

Zamu kawo bayanai kai tsaye kan yadda fadan ke gudana a Abidjan:

Bayanai kai tsaye Bayanai kai tsaye daga BBC Hausa.
Shafin na sabunta kansa.

Sabunta

2047: Dakarun da ke biyayya ga mutumin da kasashen duniya suka amince da shi a matsayin zababben shugaban kasar Ivory Coast Alassane Outtara, sun yi ta kai hare-hare a kan yankuna da dama na babban birnin kasar Abidjan, wadanda har yanzu suke karkashin ikon Laurent Gbagbo, wanda ya ki sauka daga mulki.

2050: Wani mazaunin birnin na Abidjan ya shaida wa BBC abin da ke faruwa a garin:

2051: Yace ana jin karar harbe-harbe masu karfi a koina, kamar abubuwa suna fashewa. Fashe-fashen sun fi na jiya yawa, al'amarin abin trsoro ne.

2056: A bayanin da ya aiko mana ta shafinmu na BBC Hausa Facebook, Hafizu Ibrahim cewa ya yi, ya kamata Laurent Gbagbo ya yi murabus, domin kaucewa tashin hankali, tun da dai ba shi ya lashe zaben da a ka yi ba.

2125: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya yi kira ga Mr Gbagbo da ya sauka daga kan karagar mulki ba tare da bata lokaci ba.

2054: A yanzu mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye kan rikicin Ivory Coast, Insha Allahu za mu ci gaba a gobe.


BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.