An yi kira ga Farfesa Jega ya yi murabus

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega

A Nigeria kungiyoyi da ma daidaikun jama'a na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu a kan dage zaben 'yan Majalisar Dokokin kasar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, wato INEC, ta yi jiya saboda matsalolin kayan aiki.

Martani na baya-bayan nan shi ne wanda ya fito daga Hukumar Kare Hakkin bil-Adama ta Kasa, wadda ta bukaci shugaban hukumar zaben, Farfesa Attahiru Jega, ya yi murabus nan take.

Hukumar ta bayyana a cikin wata sanarwar da ta fitar cewa bai dace Farfesa Attahiru Jega ya ci gaba da kasancewa a kan kujerar shugaban hukumar zaben ba saboda dage zabukan na jiya.

Sanarwar, a cikin kakkausan lafazi, ta ce shugaban hukumar zaben ya sanya Najeriya ta yi wani babban abin kunya duk da makudan kudaden da aka baiwa hukumar tasa don ta shirya zabukan—kudaden da Hukumar Kare Hakkin bil-Adaman ta ce sun kai dala miliyan dubu daya.

Sakataren zartarwa na hukumar, Ronald Ewubare, wanda shi ne ya bayar da sanarwar, ya ce akwai isassun masu ilimi a hukumar zaben wadanda za su iya ci gaba da aikin idan Farfesa jega ya yi murabus.

“Amma kada ka yi mani mummunar fahimta; Farfesa Jega dattijon kwarai ne, mutum ne mai ilimi sosai, kana hazikin shehun malamin siyasa, amma idan batun tafiyar da zabe ake yi, ba shi ne mutumin da ya dace ba”, in ji Mista Ewubare.

Mista Ewubare ya ce kamata ya yi Farfesa Jega ya mika mukamin ga jami’i mai binsa a girman mukami.

Wannan hukuma dai gwamnati ce ke ba ta kudin gudanarwa kuma ita ke iko da ita, abinda ya sanya wasu ke cewa gwamnati ce ke amfani da hukumar domin cimma wani buri game da zaben.

Amma Sakataren Zartarwar hukumar ya ce: “Wannan wani irin ra’ayi ne mai ban takaici.

“Ni ba mutum ne da zai mika wuya ga matsin lambar gwamnati ba”.

Mista Roland Ewubare ya kuma ce ko da yake gwamnati ce ke ba hukumar tasu kudaden gudarnawa, cin gashin kanta take yi bisa doka da kuma shelar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a Vienna, kasar Austria.

Sai dai kuma mataimakin daraktan watsa labarai a hukumar ta INEC, Mista Nick Dazang, ya ce ko da yake kowa na da ’yancin bayyana ra’ayinsa, batun shugaban ya sauka a yanzu bai taso ba domin kuwa shugaban na bayyana wa ’yan Nijeriya matakan da hukumar ke dauka dalla dalla—ya kan bayyana matsala a inda aka samu matsala—ba ya barin ’yan Najeriya cikin duhu.

Jama'a da dama dai na cewa dage zaben na jiya na janyo masu asara ta fuskoki da dama saboda kasuwanni sun kasance a rufe kuma an takaita zirga-zirgar mutane.

Su ma 'yan siyasar da aka dage zaben nasu na cewa dagawar ta sa sun tafka asara ba karama ba, saboda kowanne dan takara ya aike da wakili zuwa ko wacce rumfar zabe, kuma yawancin mazabun kasar na da darurun rumfuna a karkashinsu.

Tawagar Tarayyar Turai mai sa ido a kan zaben ma ta fitar da wata sanarwa dangane da zaben da aka dage zuwa ranar Litinin.

Tawagar ta yabi yadda jama'ar kasar suka nuna matukar sha'awa da kwarin gwiwa a kan zaben, amma ta ce ta hango cikas wajen raba kayan aiki, musamman muhimman kayan gudanar da zaben.

Karin bayani