Zaben 'yan Majalisun Tarayya a Najeriya

Inec
Image caption Hukumar zaben dai ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaben

Ba lallai zaben 'yan majalisar dokoki a Najeriya ya ja hankalin masu kada kuri'a a kasar ba, amma dai duk wanda ya samu nasara a zaben, tabbas zai samu kudaden alawus-alawus fiye da dala miliyan daya a kowacce shekara wato naira miliyan 150.

Idan ka tambayi 'yan Najeriya shin wanene me wakiltarsu a Majalisar wakilai ko ta Dattawa, yawanci basu sani ba. Kuma me 'yan majalisar ke musu? Duk za ka samu amsa guda ce:

"Yawancinsu na wajen ne don son zuciyarsu, basa kishin talakawa" In ji Ibrahim Lasisi wani mai gadi a Legas.

Lasisi ya kara da cewa: "Idan ka zabi mutum bayan yakin neman zabe, ba zaka kara ganin shi ba. Za ka ga 'yan sanda shida na gadinsa duk inda za shi. Don haka ba sa tabuwa."

Albashin 'yan Majalisar Dattijai kamar yadda gwamnati ta bayyana shi ne naira miliyan daya da dubu dari hudu a kowanne wata ba tare da an cire haraji ba wato dala dubu tara.

A yayin da kowanne dan Majalisar wakilai ke karbar naira miliyan daya da dubu dari daya, galibin ma'aikata 'yan Najeriya da suka tasamma miliyan dari da hamsin a kidayar da aka yi, suna samun kusan dala biyu ne a kowanne yini.

Sai dai kamar yadda wata cibiya mai zaman kanta mai suna Nigeria Policy and Legal Advocacy Center (PLAC) ta bayyana, 'yan Majalisar Dattijai su 109 na karbar alawus na naira miliyan sittin da uku a kowane watanni uku, sai 'yan Majalisar wakilai su 360 masu karbar naira miliyan arba'in da biyar a kowanne watanni uku.

"Basa bayyana yadda suke kashe kudaden, da zarar sun karbi kudadensu, sai su yi layar zana" in ji Clement Nwankwo wani Lauya a cibiyar PLAC.

Ya kara da cewar "suna barnata dukiyar al'umma".

'Yan Majalisa da dama wadanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tuntuba sun ki yin bayani a kan albashin na su.

Daya daga cikin 'yan Majalisar wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce: "Ina ruwanka da albashinmu, muna yi musu aiki ne".

'Kasaitaciyyar Rayuwa'

Mutane da dama suna taruwa a gaban gidaje da ofisoshin 'yan majalisa idan sun dawo daga Abuja, inda jama'a ke neman taimako don su biya kudaden haya da kudin makarantar 'ya'yansu.

A ganin 'yan Majalisar bada taimakon wata hanya ce ta ci gaba da samun goyon bayan jama'ar mazabunsu.

Sai dai albashi da alawus na 'yan Majalisa ya fara janyo suka daga ma'akatar kudi da babban bankin kasar da kamfanonin masu zaman kansu bisa fargabar hakan zai kara yawan kudaden ruwa da bankuna ke karba a kasar.

'Yan majalisa a wannan watan sun kara naira biliyan dari bakwai da arba'in da shida akan kasafin kudin 2011 da shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar a Disamba, kuma rabi daga ciki za su tafi ne kan kudaden gudanarwa na tafiyar da gwamnati.

A cewar Frank Nweke shugaban kungiyar taron tattalin arziki a Najeriya: "ba zai yiwu ba 'yan majalisa su cigaba da tafiyar da rayuwa irin haka duk da kuncin da kasar ke ciki".

Ministan kudin kasar Olusegun Aganga ya bayyana kasafin kudin da 'yan majalisa suka yiwa kwaskwarima a matsayin "wanda ba za a iya zartarwa ba".

Gwamnan babban bankin kasar Sanusi Lamido Sanusi a watan Disamban bara, ya bayyana cewar kashi ashirin da biyar cikin dari na kudaden gudanarwa na kasafin kudin kasar ana kashewa 'yan majalisa ne, abinda yasa 'yan majalisar suka gayyace shi don ya kare kansa.

Akalla 'yan Majalisar kashi tamanin cikin dari ba za su dawo ba, bayan zaben ranar Asabar abinda ya kara zafafa takarar.

Amma albashi da alawus din da zasu karba idan sun lashe zaben, bai kai yawan kudaden da suka kashe ba.

Bugu da kari ana zargin baiwa 'yan Majalisa toshiyar baki idan ana da bukatar hanzarta amincewa da wani kudirin doka.