Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zabuka a yankunan karkara a Najeriya

A Najeriya a lokuta irin na yanzu da zabukan kasar suka matso 'yan siyasa kan karade sassan kasar domin neman goyon bayan masu zabe inda wasun su kan yiwa jama'a alkawarurukan magance musu matsalolin su na inganta rayuwa tare da raba musu kudade da sauran wasu abubuwa don neman kuri'unsu.

Amma bayan jama'ar sun zabe su wasu 'yan siyasar kan gaza wajen cika alkawarurrukan da suka yiwa jama'ar har zuwa lokacin wani zaben kuma su sake komawa ga jama'ar don neman kuri'unsu.

Sai dai kamar yadda za ku ji a rahoton da wakilinmu Muhammad Annur Muhammad ya hada mana idan bera da sata to daddawa ma da wari.