Jami'an Scotland sun yiwa Koussa tambayoyi

Moussa Koussa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tsohon Ministan Harkokin Wajen Libya, Moussa Koussa

'Yan sandan yankin Soctland wadanda ke bincike a kan tarwatsa jirgin saman fasinja a samaniyar Lockerbie sun yi wa tsohon ministan hulda da kasashen wajen Libya, Moussa Koussa, tambayoyi.

Da ma dai an yanke wa wani babban jam'in leken asirin Libya hukunci dangane da tarwatsa jirgin da aka yi a shekarar 1988.

Ana kuma kyautata zaton cewa Moussa Koussa ma babban jami'in leken asirin Libya ne a wancan lokacin.

Fatan hukumomin yankin na Scotland dai shi ne manyan jami'an gwamnati wadanda suka juya wa Kanar Gaddafi baya za su taimaka masu wajen gano ko su wanene suka bayar da umarnin kai harin na Lockerbie.