Kai tsaye: Zaben 'yan Majalisun Tarayya

Zaben 'yan Majalisun Tarayya kai tsaye
Image caption Wannan ne karo na farko a cikin zabukan da za a yi

Yau take zaben majalisun dokoki a Najeriya, inda za a zabi 'yan majalisar dattijai 109 da kuma 'yan majalisar wakilai 360.

Sashen Hausa na BBC Hausa zai kawo muku bayanai kai tsaye dangane da yadda zabukan ke wakana a duk fadin Najeriya.

Za ku iya aiko mana da yadda al'amura suke wakana a yankunanku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook ko kuma ku aiko mana hotuna da bidiyo ta wannan rariyar likau din: http://www.bbc.co.uk/hausa/yourpics/

13:43 A yanzu mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye, amma za ku iya sauraren shiri na musamman da za mu gabatar muku a rediyo da misalin karfe uku na yamma. Ba ya ga wannan za kuma ku iya ci gaba da tafka muhawara a dandalinmu na sada zumunta wato bbchausa Facebook. Za kuma mu sake gabatar muku da bayanan kai tsaye a ranar Litinin da za a sake gudanar da zaben 'yan majalisun tarayya.

13:34 A gaskiya dage zabe da hukumar zaben Najeriya ta yi ya yi daidai, domin kuwa bisa ga rahotanni dake bayyana sun nuna cewa akwai makarkashiyar magudi, ALLAH ya taimaki Farfesa Jega a kan manufofinsa na gaskiya da amana. Daga Kamisu Shehu Jihar Bauchi.

13:26 Rahotannin da muke samu daga sassa daban-daban na Najeriya, na nuna cewa jama'a da dama sun nuna rashin jin dadi game da matsalolin da aka samu wadanda suka kai ga soke zaben baki dayansa.

13:22 A sakon da ya aikomana ta Facebook, Mudassir Sani, cewa ya yi Allah ya sa haka shi yafi zama alheri amma gaskiya ba mu ji dadin soke wannan zabeba, don har mun shirya tsaf.

13:14 Ina kira ga jama'ar Najeriya da mu yi hakuri mu sake fitowa zabe ranar Litinin. Daga Haliru Sani

13:09 A gaskiyadaga zabe da akayi da kwana biyu a najeriya bashi bane mafuta, domin kuwa a baya an kara wata biyu amma ba'a samu biyan bukata ba. Daga Khamusu Shehu Gamawa Bauchi.

13:02 Ana cikin tantancemu sai kawai muka ga 'yan sanda suna nade kayan aiki, wai an fasa zabe. Anya akwai gaskiya a al'amarin nan kuwa? Daga Mohammed Jalingo.

1258 Ina kira ga 'yan Najeriya da su kara hakuri da abinda ya faru, sakamakon dage zaben da aka yi a yau. Allah ya taimaki masu gaskiya. Daga Sanusi Musa Chimas, Malufashi-Katsina

1249 Rahotanni daga jihar Gombe, na cewa jama'a sun yi zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da matakin da aka dauka na soke zaben 'yan Majalisar Dattawa a jihar. 'Yan sanda sun yi amfani da barkonan tsohuwa wajen tarwatsa masu zana-zangar, sannan suka kama mutum guda i zuwa yanzu.

1238 An dage zabe zuwa ranar Litinin 4 ga watan Aprilu. - Attahiru Jega

1237 Na yi alkawarin shaida wa 'yan Najeriya duk wata matsala da aka fuskanta a zabe. Abubuwa ba su gudana yadda ya kamata ba a zabukan. Rashin isowar kayan zabe a kan lokaci. - Attahiru Jega

1235 Shugaban hukumar zabe Attahiru zai yi wa 'yan kasa jawabi kan matsalolin da ake fuskanta a zaben yau.

1233 Hoton bidiyo kan tantance masu kuria: http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110402_accreditation_video.shtml

1226 Hotuna kan tantance masu kada kuria: http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110402_accreditation_voter.shtml

1221 Kwamishinan zabe na jihar Akwa Ibom, ya shaida wa kamfanbni dillancin labarai na Reuters cewa: "Ina da katikan kada kuri'a na 'yan majalisar tarayya, amma babu takardun sakamako. Ina da takardun sakamakon majalisar Dattawa, amma babu takardun kada kuri'a. "Ina ganin ya kamata a dage wannan zaben zuwa wani lokaci, domin ba zan iya gudanar da zabe mai adalci ba a haka".

1218 Wakilinmu Muhammad Annur Muhammad ya ce a kananan hukumomin Jamaare da Itas Gadau, yanzu haka ba inda kayan zabe suka kai. A karamar hukumar Kiyawa komai na tafiya daidai, sai dai aikin tantance masu zaben na daukar dogon lokaci wanda ke sanya fargabar cewa ta yiwu ba za a iya fara zaben da karfe 12:30 ba, kamar yadda aka tsara. Kayan zabe ba su kai mazabu ba a Dutse babban birnin jihar Jigawa har zuwa karfe tara. A Hadejia, tantancewa na daukar dogon lokaci kafin a yi. A Ringim kuma akwai rahotannin tashe-tashen hankula.

1200 Aliu Baba ya ce, Bawani alamun jefa kuriya a garin bidda jihar niger state.

1200 Mu fa a Kafin Madaki, Jihar Bauchi, har yanzu, karfe sha biyun rana, ba Jami'an zabe, ba kayan zabe. Muna cikin wani hali! - Daga Lawan Abubakar

1155 Yanzu karfe 11:40am na rana har yanzu babu jami'an zabe da kayan zabe a garin Akwanga jihar Nasarawa. Daga Usman Muh'd Akwanga jihar Nasarawa

1154 Gaskiya a Gwangwazo, cikin Karamar Hukumar Birni, komai yana tafiya daidai yanda ake bukata ana ta tantance mutane cikin nutsuwa ba tashin hankali. Daga Abba Sarki Aliyu

1149 Wakilinmu Ishaq Khalid a Bauchi ya ce yanzu ne kayan aiki ke isa wasu mazabu a jihar Bauchi. Akasarin mazabu na ci gaba da jira. A Jihar Pilato kuwa alamu sun nuna ba a kai ga fara tantance masu zabe ba, yayinda a Gombe aka fara tantance masu zabe a wurare da dama. Tuni dama hukumar zabe a jihar ta dakatar zaben 'yan majalisun dattijai a jihar.

1140 A gaskiya anan birnin Patakwal akwai wurare da dama da kayan zabe basu sami isaba, kamar Rumoula da Elelewon da Bori na yankin Ogoni. Daga S Muhammad Sule Natiti

1138 Wakilinmu Umar Elleman a Lagos ya ce an fara tantance masu kada kuria a sassa dabam-daban na jihar. Sai dai ya lura cewa a wasu mazabun mutane ba su fito sosai ba.

1137 Kamfanin dillancin labarain na Reuters ya rawaito cewa an ji harbe-harben bindigogi a yankin Ekeremor na jihar Bayelsa dake yankin Niger Delta mai arzikin mai inda ake fama da rikici. Sai dai babu wanda ya samu rauni.

1131 An tantance ni, yanzu zabe nake jira kuma aiki yana tafiya dai-dai a unguwar Atafi Hadejia jihar Jigawa. Sako daga Ibrahim Musa Atafi

1130 Nura Mai Lemo ya ce Mu dai matsalar da take faruwa a mazabar Fagge dake Kano sai kaga wakilan jam'iyyu sun kawo mutane sun ce sai an tantancesu bayan ga mutane a kan layi suna jira.

1130 Alhamdulillahi mu kam a mazabar Hotoron Arewa komai na tafiya a cikin tsanaki ba tashin hankula sai dai dan abinda ba za a rasaba shi ne yadda zaben ya gudana cikin rashin sauri. Daga Umar Muh'd Ferere Hotoron Arewa Kano

1119 Alhamdulillah, mu dai anan Funtua sai godiya domin kuwa aikin zabe ya kankama kamar yadda aka alkawarta. Fatana a yi zabe cikin kwanciyar hankali. Sakon Saidu Ikara

1117 Mu dai nan a kwanar Dangora mazabar Yalwa karamar Hukumar Kiru Kano, sai yanzu kayan aiki suka iso, kuma a gaskiya ana samun matsala wajan tantancewa.

1117 Bayanai daga sassa daban daban na Najeriya na nuna cewa yayinda aikin tantance masu zaben ke tafiya yadda ya kamata a wasu yankuna, a wasu kuma ko kayan aiki ma ba a kai ba.

1111 Musa Abdurrahmanya rubuta a shafinmu na BBC Hausa Facebook "To yau fa da yardar Allah azzalumai za ku fara sanin matsayinku, za ku tafi, kasa za ta samu zama lafiya da ci gaba. Talakawa za su samu 'yancinsu. Alhamdulillah

1110 Mu a jihar Bauchi karfe 10:55, ba mu ga kayan zabe ba a gidan Yaya. Daga Habu Mai Walda.

1103 Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kwara ta soke dukkan zabukan 'yan majalisar dokoki a jihar.

1101 Sade Saidu Daura A gaskiya mu dai nan Daura komai na tafiya yadda ya kamata. Musamman yadda jama'a suka bada hadin kai wajen nutsuwa akan layi wajen tantance sunayen masu kada kuri'a.

1100 A gaskiya Jega sai an sake shirin zabe domin tantancewar nan akwai matsala mutane na shan wahala. Daga Sagir Adamu compound Malumfashi.

1057 Bayanai daga jihar Kwara na nuna cewa hukumar zaben kasar ta dakatar da zabuka a wasu mazabu na jihar.

1055 Mallam Abubakar daga Karamar Hukumar Gumbi jihar Adamawa, ya ce mutane sun fito tun karfe 7, sun yi tururuwa amma har yanzu babu alamar jami'an zabe.

1050 Malam Barkindo daga Yola jihar Adamawa: har yanzu ba kayan aiki a mazabu da dama na jihar Adamawa.

1046 A halin yanzu komai yana tafiya game da tantance masu kada kuri'a. Domin Akwai akwatina guda biyar wadanda layukan suna tafiya anan mazabar "Gama Tudu Brigade, Kamar Hukumar Nassarawa jihar Kano. Daga Murtala Ibrahim Ahmed

1046 Bilal daga Sokoto. Mu kan kayan aiki sun iso a mazabarmu a daidai lokaci, kuma tantance masu jefa kuri'a na tafiya lahiya lau, amma bamu da jami'an tsaro ko guda a mazabar a makarantar waziri modal Primary a Sokoto.

1041 Har ya zuwa yanzu ba ma'aikatan hukumar zabe a mazabar Sani Mainagge dake karamar Hukumar Gwale a jihar Kano, jama'a da dama sun nuna rashin jin dadinsu musamman dake sun fito da wuri domin tantance su. Sako daga Ayatullahi Yammamman.

1040 Lallai ina murna da wannan lokaci mai tarihi ar ayuwata, wanda zan fara zabe a karon farko, ina dan shekara 19 da wata 7. Ibrahim Kacallu KC unguwar Mangawan Birniwa, Jigawa

1017 Za ku iya aiko mana da yadda al'amura suke wakana a yankunanku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook ko kuma ku aiko mana hotuna da bidiyo ta wannan rariyar likau din: http://www.bbc.co.uk/hausa/yourpics/

1015 Dr Kabir Abdul daga jihar Naija ya ce har yanzu a mazabar da yake ba a kawo kayan aiki ba.

10:15 A sakon da ya aiko mana ta wayar tarho daga Kano, Bako Gwammaja ya ce tuni aka riga aka tantance shi, kuma a yanzu yana jira ne kawai a fara kada kuri'a domin ya kada tasa.

1007: Zahraddeen Ibrahim Arzai ya rubuta a shafinmu na Facebook cewa, a yanzu haka a Arzai mazaba ta aikin tantancewa yana tafiya kamar yadda ake tsammani.

10:05 Da alama dai labarin kusan daya ne a sassa daban-daban na Najeriya, kayan aiki ba su isa rumfunan zabe ba a kan kari.

10:02 Abdulkarim Musa: Ya rubuta a shafinmu na BBC Hausa Facebook "Wannan shi ne adalci? Mu karamar hukuman Lere a jihar Kaduna har yanzu ba kayan aiki.

09:46 Zakari Adamu shugaban rundunar adalci ta jihar Yobe, Mazabar Hausawa Asibiti, a garin Potiskum babu kayan aiki har yanzu.

0945 Yakubu Yusufu Fufure Michika jihar Adamawa ya ce, yana mazabar Kwarfi, kuma har yanzu babu akwatin zabe ko kayan aiki. Jama'a sun damu.

09:30 Habibu Abdulhamid daga Wukari jihar Taraba ya ce i zuwa yanzu babu alamar kayan aiki ko jami'an zabe a wasu mazabun jihar.