Martani dangane da sake dage zaben 'yan majalisu

Zabe a Najeriya
Image caption 'Yan siyasa a Najeriya da sauran al'umma na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da sake dage zaben 'yan majalisun dokoki zuwa ranar asabar mai zuwa

A Najeriya, al'ummar kasar na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da matakin hukumar zaben kasar na sake dage zaben majalisar dokokin kasar zuwa ranar asabar dake tafe.

Wannan dai shi ne karo na biyu da hukumar zaben ta INEC ta dage zabukan a cikin mako guda sabo da matsalar tanade-tanaden kayan aiki.

Yayinda wasu 'yan siyasa a najeriyar ke nuna cewar gwiwarsu ba ta yi sanyi ba dangane da shiga zaben, wasu jam'iyyun adawar kasar kuwa na cigaba da nuna damuwa kan yiwuwar sake aukuwar kuran kuran da aka fuskanta a ranar asabar din data gabata.

Jam'iyyun sun yi kukan cewa an samu matsaloli da dama a ranar zabe, ciki kuwa har da rajistar masu kada kuri'a inda suka ce wasu jama'a basu ga sunayensu ba.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ce a shirye take ta magance wannan matsalar.

Jam'iyyar PSP ma, ta bayyana rashin gamsuwarta game da dage zabukan, inda shugaban jam'iyyar Dr. Junaidu Muhammad ya shaidawa BBC cewar hukumar zaben kasar ba ta taka rawar gani ba.