Shugaba Gaddafi na neman mafita in ji Girka

'Yan tawayen kasar Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kasar Girka ta bayyana cewar shugaba Gaddafi na Libya na neman mafitar rikicin daya dabaibaye kasar

Kasar Girka ta bayyana cewa, wani wakilin Kanar Gaddafi ya shaida mata cewa, shugaban Libya na neman mafitar rikicin kasar.

Wakilin wato Abdul-Ati al-Obeidi, wanda tsohon Fira Minista ne, ya sadu da Fira Ministan kasar ta Girka ne wato George Papandreou a birnin Athens da yammacin jiya Lahadi.

Bayan tattaunawarsu, ministan kula da harkokin wajen kasar ta Girka Dimitris Droutsas ya shaidawa manema labaru cewa daga jawabin wakilin Libyan, ta bayyana cewa gwamnatin na neman mafita.

Yace akwai bukatar daukar kwakkwaran matakin zaman lafiya, da kwanciyar hankali a yankin, kuma Girka za ta yi kokarin samar da zaman lafiyar.