Jam'iyyar ACN ta baiwa INEC shawara

Jam'iyyar ACN ta baiwa INEC shawara
Image caption ACN na daga cikin jam'iyyun da suka nemi a kara dage zaben

Jam'iyyar adawa ta Action Congress of Najeriya ta gabatar da wasu kwararan shawarwari ga Hukumar zaben kasar, domin shawo kan matsalolin da aka fuskanta.

Jam'iyyar ACN ta ce daukar wannan matakin, wata dabara ce da Hukumar INEC za ta yi amfani da ita dan kaucewa irin matsaloli da aka fuskanta a zaben 'yan Majalisun dokoki da aka daga zuwa ranar Asabar.

A cewar babbar jam'iyar adawar, dole ne hukumar zabe ta zama ta yi karatun na nutsu dan kaucewa wani abu da zai haifar da zubewar kimar Najeriya.

Kasar da ake wa ganin manyan zabububbkan ta biyu a baya wato na shekara ta 2003 da kuma 2007 sun fuskanci suka daga kungiyoyin kare hakkin bil'adama da Turai da Amurka. Bisa magudi da rikice-rikice.

'Da ba mu samu kanmu cikin matsala ba'

Shugaban ACN reshen jihar Lagos Cif Henry Ajemole ya aikewa hukumar zabe cewa akwai wasu manyan batutuwa da lalle Hukumar za ta kawo gyara dan kaucewa akasin da aka samu a ranar Asabar da ta gabata.

Sai dai jam'iyyar ACN ta ce kamar yadda aka kira hukumar zabe mai cin gashin kanta to lalle ya kamata ta amsa wannan sunan na sanya lokaci da ranakun zabe ba tare da sa hannun wasu daga waje ba.

Ya ce: "Lallai da an baiwa hukumar zabe ta fito da ranakun zabe, a maimakon Majalisar Dokoki ta tarraya ta bayar da ranakun zaben. To lalle da ba za mu tsinkayi kanmu cikin matsalar da ta faru ba".

Jam'iyyar ACN ta ce cikin shawarwari da ta aikewa hukumar INEC dan kaucewa akasin da aka samu sun hada da tabbatar da kayayyakin zabe sun isa cibiyoyin zabe a fadin kasar cikin lokaci.

Tabbatar da jami'an hukumar INEC sun isa guraban gudanar da zabe tare da kayayyakin zabe a lokaci guda.

Da kuma tabbatar da duk wadanda suka yi rijista sun kada kuri'a koma baya abinda aka shaida wasu mutane sun gaza kada kuri'a a sakamakon akasin sunayen su a rubuce.

Cif Henry Ajemole ya ce wannan shi ne daya daga cikin dalilanmu na aikewa da shawarwari ga Hukumar INEC dan ta saurari shawarwarin mu.

Jam'iyyar ta ce idan ba a aiwatar da tsare-tsaren da za su kawar da matsalolin da aka fuskanta ba, to za ta garzaya kotu.