Ana cigaba da tafka kazamin fada a Abidjan

Sojoji a Kasar IvoryCoast Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana cigaba da tafka kazamin fada a babban birnin kasar IvoryCoast na Abidjan

Ana cigaba da samun rahotannin dake nuna cewar ana can ana tafka kazamin fada a babban birnin kasar Ivory Coast na Abidjan.

Dakarun dake yin biyayya da mutumin da kasahen duniya suka amince shine ya lashe zaben shugabankasar da aka gudanar, Alassane Outtara na gwabza fada da sojojin shugaba Laurent Gbagbo, wanda yaki amincewa ya sauka daga kan kujerar mulkin kasar.

Anji karar harbin manyan bindigu cikin dare a kusa sa gidan talabijin din birnin da kuma harabar fadar shugabankasar, Laurent Gbagbo.

A cikin daren, wani mai magana da yawun Mista Outtara yace sojojinsu sun kwace fadar shugabankasar. Sai dai ba a kaiga tabbatar da wannan labari ba, da ma inda Shugaba Gbagbon yake a yanzu haka