'Yan tawayen Libya sun zargi dakarun kungiyar NATO

'Yan tawayen kasar Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen kasar Libya sun ja hankalin dakarun kungiyar NATO akan kashe kashen fararen hular da sojojin gwamnati ke cigaba da yi a Misrata

Jagoran 'yan tawaye a Libya Abdulfatah Yunis, ya zargi dakarun kungiyar tsaro ta NATO da komawa gefe su na kallo alhali dakarun Kanal Gadaffi na ci gaba da kashe mutane a garin Misrata, inda aka yiwa kawanya.

Janar Yunis ya ce idan har dakarun kungiyar NATO suka bata lokaci ba tare da sun dau wani mataki ba, to kuwa yace za a shafe al'ummar garin Misratan gabakidaya.

Ya kara da cewar kungiyar NATO ta basu kunya. Abdulfatah Yunis yace shi da sauran hafsoshinsa yanzu haka suna cigaba da tuntubar wakilan NATO domin su kai hari, don kare fararen hula.

To amma yace NATO ba ta basu abinda suke bukata ba.