An hallaka wasu 'yan makaranta a Brazil

Wata mata a bakin asibitin da aka kai wadanda aka harbe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata a bakin asibitin da aka kai wadanda aka harbe

Wani dan bindiga ya harbe har lahira yara akalla 11 a wata makaranta a birnin Rio de Janeiro na Brazil.

Yansanda sun ce ya shiga cikin ginin yana dauke da bindigogi biyu da kuma wata wasikar kunar bakin wake , sannan ya kashe kansa a lokacin da jami'ai suka tinkare shi.

Mutane akalla 20 ne da suka hada da malamai da dalibai aka jikkata a harbin.

An dai bayyana makashin a matsayin wani tsohon dalibin makarantar.

Shugaba Dima Rousseff ta zubar da kwalla yayinda ta yi Allah waddai da kisan gillar.