Babban Bankin Turai ya kara kudin ruwa

Babban Bankin Turai ya kara ainihin kudin ruwansa a karon farko tun shekara ta dubu 2 da 8 da maki 25 na kasuwanci.

Bankin wanda yake da rassa a kasashe 17 dake aiki da kudin tarayya na Euro, ya saka kudin ruwan ne daga rubu'in kashi daya cikin dari zuwa kusan kashi biyu.

Shugaban Bankin, Jean -Claude Trichet, ya ce matakin ya wajaba saboda haduran da ake da su a halin yanzu dangane da daidaituwar farashi a kasashen da ke amfanin da kudin Euro.

Ya ce karin zai sauko da farashin kaya -- wanda a halin yanzu ya zarta kashi 2 da rabi cikin dari wato kasa ko kuma kusa da burin babban bankin Turan na samun kashi 2 cikin dari.