Wasu 'yan Kenya sun yi karar Birtaniya

Wau tsofaffi 4 yan kasar Kenya sun yi karar Gwamnatin Birtaniya game da zargin cewar an gana masu akuba a lokacin murkushe boren Mau Mau a Kenya a shekarun alif dari tara da 50.

Lauyoyinsu sunce mutanen 4, 3 maza da kuma mace guda, na wakiltar daruruwan 'Yan Kenyar da aka kashe ko aka jikkata a lokacin boren game da mulkin mallaka.

Gwamnatin Birtaniya ta yi bayanin cewar ba ita ya kamata a dora wa laifi ba saboda Kenya ta dauki alhaki na shara'a kan wadannan keta hakkoki a lokacin da ta samu yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1963.

Sai dai daya daga cikin Lauyoyin Birtaniya dake wakiltar 'Yan Kenyar ya yi watsi da wannan da wannan madogara ta Birtaniya;

Ya ce, "muna cewa ne doka tana tare da mu, cewar alhakin abinda ya faru ya rataya ne a kan Gwamnatin Birtaniya.Saboda bai dace Gwamnatin Birtaniya ta mika miyagun ayyukan ta ga yan Kenya , ta fuskar alhakin abinda ya faru a dukanin tsawon wadannan shekaru da suka wuce ba."