An gano gawarwakin mutane 60 a Mexico

Shugaban Kasar Mexico, Felipe Calderon Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Kasar Mexico, Felipe Calderon

Mahukunta a jahar Tamaulipas dake kasar Mexico sun ce sun gano gawarwakin mutane kimanin sittin a kaburbura guda takwas da aka binne mutane da yawa a cikinsu.

Gwamnatin jihar Tamaulipas ta ce, tana gudanar da binciken ko gawarwakin mutanen na fasinjojin motar safar da gungun masu safarar miyagun kwayoyi suka sace ne, makonni biyu kenan da suka gabata.

Wakilin BBC ya ce mutane da dama sun yi amannar cewa, gawarwakinda aka gano, tamkar wani abin kunya ne ga manufofin shugaban kasar na yaki da masu safarar miyagun kwayoyi.

Manufofinda dubban 'yan kasar suka yi Allahwadai da su a lokacin da suka hau kan tituna a ranar Laraba suna cewa 'zub da jinin ya isa haka'.